Saudiyya Ta Sake Yin Kisan Kiyashi A Kasar Yemen
Jiragen yakin kawancen Saudiyya sun kashe mutane 15 da jikkata wasu fiye da 20 a kusa da garin Hudaida dake yammacin kasar Yemen
Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen ta ba da labarin cewa; An kai harin ne a jiya da dare a yankunan Farzaha San'a, da al-kashwai da suke a daure da Hudaidah.
A gefe daya ma'aikatar tsaron kasar ta Yemen ta sanar da cewa; Sojoji da kuma dakarun sa kai na Ansarullah sun mayar da martani akan wani yunkuri da 'yan koren Saudiyya su ka yi domin isa filin saukar jiragen sama na Hudaidah.
Ma'aikatar ttsaron kasar ta Yemen ta ci gaba da cewa; An kashe da kuma jikkata da dama daga cikin 'yan koren na Saudiyya. Har ila yau sojojin na Yemen sun lallata motocin yaki guda 8 na 'yan koren Saudiyyar.
Saudiyya dai ta shelanta yaki ne akan kasar Yemen tun a 2015 da zummar mayar da shugaban kasa mai Murabus Abulhadi mansur akan karagar mulki, abin da har yanzu bai tabbata ba.