An Yanke Wa Mukadashin Jagoran (IS) Hukuncin Kisa
(last modified Wed, 19 Sep 2018 16:13:49 GMT )
Sep 19, 2018 16:13 UTC
  • An Yanke Wa Mukadashin Jagoran (IS) Hukuncin Kisa

Wata kotun hukunta manya laifuka a Iraki, ta yanke wa wani mukadashin jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta IS hukuncin kisa.

Kotun ta Karkh, ta sanar da hukuncin kisa ga dan ta'addan mai suna Ismail Alwan Salmane al-Ithawi" ta hanyar rataya.

Shi dai dan ta'addan yana rike da manyan mukamai da dama a cikin kungiyar ta Daesh, a cewar sanarwar kotun.

''Salmane al-Ithawi'' ya tsere Siriya ne inda yake kulla alaka da shugabannin wasu kabilu, kafin daga bisani ya isa Turkiyya, bayan 'yantar da yankunan da dama da mayakan dake ikirari da sunan jihadi ke rike da, sannan aka cafke shi ta hanyar hadin gwiwa da hukumomin leken asirin Irakin, Turkiyya dana Amurka

A ranar 15 ga watan Fabariru ne hukumomin Irakin suka sanar da tuso keyar shi bayan cafke shin a Turkiyya,  

Shi dai Ismail Alwan Salmane al-Ithawi, shi ne ke kulda kwamitin nada sarakuna da mayan jigan jigan da kuma masu bada fatawa na kungiyar ta IS.