Palasdinu: Yahudawa 'Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Masallacin Kudus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33350-palasdinu_yahudawa_'yan_share_wuri_zauna_sun_kutsa_masallacin_kudus
Majiyar Palasdinawa ta ce; 'Yan share wuri zauna 159 ne su ka kutsa cikin masallacin kudus a karkashin kariyar sojojin sahayoniya
(last modified 2018-09-26T19:08:06+00:00 )
Sep 26, 2018 19:08 UTC
  • Palasdinu: Yahudawa 'Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Masallacin Kudus

Majiyar Palasdinawa ta ce; 'Yan share wuri zauna 159 ne su ka kutsa cikin masallacin kudus a karkashin kariyar sojojin sahayoniya

Kutse cikin masallacin kudus ya fara zama jiki inda a kowance mako 'yanhudawa 'yan share wuri zaune su ke shiga cikinsa sau daya ko sau biyu.

a gefe daya sojojin sahayoniya sun kai hari a yankuna daban-daban na yammacin kogin Jordan, inda su ka yi awon gaba da palasdinawa 15 ba tare da tuhumarsu da wani laifi ba.

Bayan kamun mutane, an yi taho mu gama a tsakanin samarin palasdinawa da kuma sojojin 'yan sahayoniya.

Da a kwai Palasdinawa 6500 a cikin kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila, 300 daga cikinsu kananan yara.