Ana Ci Gaba Da Kwashe 'Yan Gudun Hijrar Siriya Daga Labnon
Cibiyar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta sanar a jiya alhamis cewa an dawo da wata tawagar 'yan gudun hijrar dake tsugune a kasar Labnon zuwa gida
Tashar talabijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin tehran ta nakalto cibiyar dake kula da 'yan gudun hijra ta kasar Siriya na cewa cikin sa'o'i 24 da suka gabata 'yan kasar daga gudun hijra a Labnon 100 ne suka dawo kasar ta hanyar mashigar Jadeeda Yasun da Addabusiya dake kan iyakan da kasar ta Labnon.
Cibiyar ta ce ko a ranar larabar da ta gabata ma 'yan gudun hijrar 527 ne suka dawo gida, inda aka tsugunar da su a sansanin 'yan gudun hijra kafin su fice zuwa yankunan su.
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta samar da sansanin karbar 'yan gudun hijra a kasar ta Siriya ne domin sausauka komawarsu gida, ita dai wannan cibiya ita ke kula da taimakon 'yan gudun hijrar da suka dawo gida da kuma sake gida gidajensu.
A yakin shekaru bakwai na kasar ta Siriya, kimanin 'yan kasar miliyan bakwai ne suka yi hijra zuwa kasashen ketare, daga cikinsu akwai kimanin miliyan daya da rabi dake tsugune a kasar Labanon.