HKI Tana Nuna Damuwarta Akan Makaman Harbo Jiragen Sama Na Syria
Ministan yakin haramtacciyar Kasar Isra'ila Avigdor ne ya nuna damuwa akan shirin kasar Rasha na bai wa Syria makaman kakkabo jiragen sama samfurin S-300
Sai dai Ministan yakin na haramtacciyar kasar ta Yahudawa Lieberman ya ci gaba da cewa; Babu wata mafita a gaban Isra'ila idan ba ci gaba da kai wa Syria hari ba.
Ra ranar Talatar da ta gabata ne dai ministan tsaron kasar Rasha Sergey Shoygu ya sanar da cewa; Kasarsa ta kammala mikawa Syria makaman na s-300.
A cikin watan Disamba ne dai haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wani hari a cikin kasar syria wanda ya yi sanadin faduwar jirgin leken asiri na kasar Rasha.
Rasha ta dora alhakin faduwar jirgin yakin nata akan haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da yin alkawalin bai wa Syria makaman S-300