Labanon : 'Yan Gudun Hijirar Siriya Za Su Koma Gida
Labanon ta ce adadin 'yan gudun hijirar Siriya da za su koma gida ya zuwa karshen shekarar nan ya kai 100,000.
Da yake bayyanawa masu aiko da rahotanni hakan, Shugaban hukumar tsaron kasar Lebanon, Abbas Ibrahim ya ce, hukumar na bada tsaro da mafaka, baya ga yafiyar haraji ga 'yan gudun hijirar dake zaune a kasar ba bisa ka'ida ba, domin gaggauta komawarsu gida.
Ya ce hukumomin tsaron Labanon din na aiki da hukumar MDD mai kula da 'yan gudun hijira domin tabbatar da mutanen sun koma gida lafiya, kuma bisa radin kansu.
Ya kuma yabawa yunkurin hukumomin Rasha dangane da aikin.
Domin mayar da 'yan gudun hijirar kasarsu, Rasha ta gabatar da wani kuduri ga hukumomin tsaron Lebanon, wanda ke da nufin tabbatar da komawar 'yan gudun hijira 890,000 zuwa Siriya.