Haramtacciyar Kasar Isra'ila Na Ci Gaba Da Kame Palasdinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33650-haramtacciyar_kasar_isra'ila_na_ci_gaba_da_kame_palasdinawa
Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki a yankuna daban-daban na yammacin kogin jordan inda su ka yi awon gaba da palasdinawa 15
(last modified 2018-10-16T12:12:21+00:00 )
Oct 16, 2018 12:12 UTC
  • Haramtacciyar Kasar Isra'ila Na Ci Gaba Da Kame Palasdinawa

Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki a yankuna daban-daban na yammacin kogin jordan inda su ka yi awon gaba da palasdinawa 15

Tashar talabijin din al-alam ta ba da labarin cewa a yau talata, sojojin na Sahayoniya sun kai farmaki zuwa garuruwan qalqiliya, Ramallah, Kudus, da al-khalil da suke a yammacin kogin Jordan.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Sojojin na Sahayoniya sun kuma jikkata wasu paladinawa 19 a lokacin Zanga-zangar da suke yi ta kare hakkin komawa gidajensu na gado.

Wani jami'in kungiyar 'yanto Palasdinu Mahir Mazhar ya bayyana cewa; Sai idan an dauke takunkumin da aka kakabawa yankin na Gaza ne, palasdinawa za su dakatar da Zanga-zangar da suke yi domin tabbatar da hakkinsu na komawa gidajensu na gado da a ka kore su daga ciki, yayin kirkirar haramtacciyar kasar Isra'ila.

Tun a 2006 ne aka killace yankin na Gaza ta sama da ruwa da kasa, abin da ya mayar da yankin zama wani kurkuku.