Kwamandan NATO Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Afganistan
(last modified Thu, 18 Oct 2018 15:59:30 GMT )
Oct 18, 2018 15:59 UTC
  • Kwamandan NATO Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Afganistan

Rahotanni daga Afganistan na cewa kwamandan kungiyar tsaro ta NATO, Janar din sojin Amurka, Scott Miller, ya tsallake rijiya da baya a wani harin bindiga da kungiyar taliban ta dauki alhakin kaiwa a yankin Kandahar.

An dai kai harin ne yau Alhamis a wani taro kan sha'anin tsaro gabanin zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Afganistan, wanda janar Miller ke halarta.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutum uku ciki har da shugaban ma'aikatar tsaro na yankin Kandahar Janar Abdul Raziq, da kuma raunana mutane 12 ciki harda gwamnan yankin da kuma wasu sojin Amurka uku.

Bayanai daga yankin sun ce gwamnan yankin Zalmai Wesa na cikin mawuyacin hali.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, maharin wani mai tsaron lafiyar gwamnan yankin na Kandahar ne.

Shi dai janar Abdul Raziq na ma'aikatar tsaron yankin na kandahar ya yi kaurin suna wajen daukar matakan ba sani ba sabo ga 'yan kungiyar ta Taliban, kuma wannan ba shi ne karon farko da kungiyar ke yunkurin hallaka shi ba.