Shugaba Asad Na Siriya Ya Soki Lamirin Kasashen Yamma
Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya ce wasu daga cikin kasashen yankin da kasashen Yamma na ci gaba da yin katsa landan kan al'amuran siyasar kasar.
A yayin da yake ganawa da manzon musaman na Shugaban kasar Rasha kan kasar Siriya Alexander Lavrentiev a wannan juma'a, Shugaban kasar Siriya ya nuna takaicinsa kan yadda wasu kasashen yankin da kuma kasashen Yamma ke ci gaba da yin katsa landan a harakokin siyasar kasar.
Shugaba Asad ya ce kasarsa na hada kai ne da kasashen da suke taimakawa kasar da kasar wajen kawo karshen 'yan ta'adda da ta'addanci, kuma za ta ci gaba da kare hakin kanta bisa shawarwarin kasa da kasa, sannan kuma ba za ta amince da katsa landan na wasu kasashe game da harakokin cikin gidan ba.
A bagare guda kuma Shugaba Asad ya bayyana cewa dawo da 'yan kasar dake gudun hijra zuwa kasashen waje gida daga cikin ayyukan da kasar ta sanya a gaba.
Shugaba Bashar ya gana da manzon musaman na shugaban Rasha ne kan mahiman batutuwan da suka shafi makomar kasar ta Siriya musuman ma kan kafa kwamitin sabunta kundin tsarin milkin kasar.