Miliyoyin Masoya Ahlulbaiti Na Tarukan Arba'in A Karbala
(last modified Tue, 30 Oct 2018 18:59:26 GMT )
Oct 30, 2018 18:59 UTC
  • Taron juyayin ranar Arba\\\'in din dai ana  gudanar da shi ne a ranar 20 ga watan Safar na kowace shekara.
    Taron juyayin ranar Arba\\\'in din dai ana gudanar da shi ne a ranar 20 ga watan Safar na kowace shekara.

A Iraki miliyoyin mabiya da masoya Ahlulbaiti (a.s) daga duk fadin duniya na taruwa a birnin Karbala don gudanar da juyayin Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da cikar kwanaki 40 da kisan gillan da aka yi wa Imam Husainin da iyalai da magoya bayansa a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s).

Rahotannin sun ce tun jiya ne dai miliyoyin mutanen suke ta isowa birnin na Karbala mafi yawansu suna tattaki daga birnin Najaf da ke kimanin kilomita 76 daga birnin Karbala din don halarta taron na Arba'in da ake ci gaba da gudanar da shi a yau din nan Talata.

Kimanin mutane miliyan 15 ne aka kiyasta suna halartar taron na ar'ba'in. 

Bayanai daga Irakin sun ce gwamnatin kasar ta dau tsauraran matakan tsaro a garin Karbala din da kewayensa da kuma dukkanin hanyoyin shigowa garin don kiyaye lafiyar masu ziyarar daga duk wata barazana.

Taron juyayin ranar Arba'in din dai ana  gudanar da shi ne a ranar 20 ga watan Safar na kowace shekara, wato kwanaki 40 bayan kisan gillan da aka yi wa Zuriyar Annabi a Karbala din a ranar 10 ga watan Muharram na shekara 61.