Ansarullah: Amurka Tana Ckin Masu Yakar Kasar Yemen
Wani Jami'i na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya ce; babu yadda Amurka za ta zama mai shiga tsakani alhali tana cikin masu yakar kasar.
Muhammad al-Bukhaiti ya fada wa tashar talabinin din al'alam a yau Laraba cewa; Ko kadan bai kamata a ce wani bangare na kasashen waje ya sa hannu a cikin yadda bangarorin al'ummar Yemen za su tattauna da junansu ba.
al-Bukhaiti ya ci agba da cewa; Tattaunawa ta zama wajibi a tsakanin al'ummar Yemen domin kai wa ga kafa gwamnati wacce dukkanin bangarorin kasar za su aminta da ita.
Tun da fari kungiyar ta Ansarullah ta yi tir da batun da ministan tsaron Amurka James Mattis ya bijiro da shi na karkatsa kasar Yemen zuwa yankuna masu kwarya-kwaryar 'yanci.
Tun a 2015 ne Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen wanda ya zuwa yanzu ya ci rayuka fiye da 13,000, wasu fiye da 50,000 kuma su ka jikkata.