Nov 19, 2018 16:34 UTC
  • Khashoggi : Jamus Zata Kakaba Wa 'Yan Saudiyya 18 Takunkumi

Ma'aikatar harkokin wajen Jamsu, ta ce kasar na shirin kakaba wa wasu 'yan Saudiyya 18 takunkumin hana shiga kasar, bisa zargin kashe dan jaridan nan Jamal Khashoggi.

Da yake sanar da hakan ga manema labarai a birnin Brussels, inda yake halartar wani taron ministocin harkokin wajen kasashen Turai, ministan harkokin wajen kasar ta Jamus, Heiko Maas, ya ce an dauki wannan matakin ne tare da hadin gwiwar kasashen Faransa da Biritaniya.

Wannan na zuwa ne bayan da a ranar Alhamis data gabata, Amurka ta sanar da kakaba wasu jerin takunkumai da suka hada dana toshe asusun kudade da kaddarorin wasu 'yan Saudiyyar su 17, bisa zargin hannu a kisan dan jaridan.

Daga dai cikin mutanen har da wasu jami'an tsaron lafiyar yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed ben Salmane, da kuma jakadan Saudiyya na karamin ofishin jakadancin Saudiyya na birnin Santambul, Mohammad Al-Otaibi, inda aka kashe dan jaridan.

Kawo yanzu dai ofishin mai gabatar da kara na Saudiyya ya sanar da cafke mutum 21, bisa zargin kisan dan jaridan, saidai ba'a bayyana sunayensu ba, amma an ce biyar daga cikinsu an yanke masu da hukuncin kisa, bisa bada umarnin kashe Jamal Khashoggi a ranr 2 ga watan Oktoba da ya gabata.

Tags