Yemen : Za'a Tattaunawa Tsakanin Masu Rikici A Watan Disamba
Amurka ta sanar da cewa za'a yi tattaunawa a farkon watan Disamba mai zuwa, tsakanin bangarorin dake rikici da juna a kasar Yemen.
Da yake sanar da hakan ga manema labarai, sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya ce kasashen Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa duk sun nuna goyan baya ga tattaunawar.
Mista Matis ya kauda yiwuwar gudanar da tattaunawar a watan Nuwamba nan, amma a cewar yana da yakinin cewa bangaren gwamnatin Yemen dake samun goyan bayan MDD, karkashin jagorancin Abd Rabbo Mansour Hadi dake gudun hijira a Saudiyya da kuma 'yan gwagwarmaya neman sauyi na Houtsis zasu samu damar shiga tattaunawar a farkon watan Disamba.
A cikin shekara 2015 ne dai Saudiyya ta shelanta yaki kan kasar ta Yemen, da nufin taimakawa gwamnatin loacin yakar 'yan Houtsis, yakin da kawo yanzu ya lashe rayukan mutane kimanin 10,000 da kuma jefa wasu miliyan 14 cikin bala'in yinwa da rayuwa mafi muni a duniya.