Nov 30, 2018 04:18 UTC
  • Yemen : 'Yan Houthis Sun Gindaya Sharadi Kafin Shiga Tattaunawa

'Yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis a Yemen, sun gindaya sharadin cewa, zasu shiga tattaunawar da za'ayi a Sweden, a shiga tsakanin MDD, muddin aka basu tabbaci akan tafiyarsu da dawowarsu tawagarsu cikin cikaken tsaro.

Duk da cewa har yanzu Majalisar Dinkin Duniyar bata fidda wata ranar da za'ayi tattaunar ba, amma Amurka ta ce tattaunawar zata gudana a farkon watan Disamba mai shirin kamawa.

Da yake sanar da hakan a shafinsa na Twitter, madugun 'yan gwagwarmayar na Houtsis, Mohammed Ali al-Houthi, ya ce, yana sa ran tawagar ta 'yan Houtsis zata isa a Sweden da yardar Allah a ranar 3 ga watan Disamba, amma da sharadin a tabbatar da tsaro kan shige da ficcen tawagar ta 'yan Houtsis.

Haka zalika al-Houthi, yana bukatar tabbacin cewa sauren bangarorin su ma da gaske suke akan samar da zaman lafiya.

Wakilin MDD kan rikicin kasar ta Yemen, Martin Griffiths, na ci gaba da nemo hanyoyin da zasu kai ga hada bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen kan teburin tattaunawa ta hanyar siyasa domin kawo karshen yakin da aka kwashe kusan shekaru hudu ana gwabzawa a wannan kasa ta Yemen, kuma wannan shi ne karo na farko da 'yan Houtsis suka bayyana anniyarsu ta shiga tattaunawar.

Yakin da kasar Saudiyya dake goyan bayan gwamnatin Abd Rabbo Mansour Hadi dake gudun hijira a Saudiyyar ta shelanta kan kasar ta Yemen, tun cikin shekara 2015 ya dai yi sanadin mutuwar mutane kimanin 10,000 da kuma jefa kasar ta Yemen cikin bala'i mafi muni a duniya a cewar MDD.

 

Tags