Kungiyar Jihadul-Islami Ta Gargadi HKK Akan Lebanon
Kungiyar gwagwarmayar Palasdinu ta Jihadul_Islami ta ja kunnen hkk akan tsonakar kasar Lebanon ko Gaza
Wakilin kungiyar ta Jihadul-Islami a kasar Lebanon Abu Samir Musa ya yi ishara da yadda 'yan sahayoniya su ka kunyata a yankin Gaza, sannan ya ce gwagwarmaya a yankin Gaza ce ta takawa sojojin Sahayoniya birki.
Abu Samir ya kara da cewa; "Yan gwagwarmaya a yankin Gaza sun tabbatar da cewa suna cikin shirin ko ta kwana domin fuskantar duk wata barazana daga 'yan mamaya
Jami'in na kungiyar Jihadul-Islami ya kara da cewa Manufar da ta sa Palasdinawa suke gudanar da Zanga-zanga a kowace juma'a shi ne tabbatar da hakkinsu na ci gaba da gwagwarmaya da neman 'yanto da dukkanin palasdinu da babban birninta zai zama Kudus
Gargadin na Jihadul-Islami dai ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Sahayoniya su ka fara rusa ramukan da su ka ce Hizbullah ta gina har cikin palasdinu da ke karkashin mamaya