Sojojin Sahayoniya Sun Kai Hari A Yankin Yammacin Kogin Jordan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34380-sojojin_sahayoniya_sun_kai_hari_a_yankin_yammacin_kogin_jordan
Sojojin na haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kuma kame samarin palasdinawa da dama a yayin harin na asubahin yau Lahadi
(last modified 2018-12-09T12:26:43+00:00 )
Dec 09, 2018 12:26 UTC
  • Sojojin Sahayoniya Sun Kai Hari A Yankin Yammacin Kogin Jordan

Sojojin na haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kuma kame samarin palasdinawa da dama a yayin harin na asubahin yau Lahadi

Garuruwan da harin ya rutsa da sun sun kunshi al-khalil, Azun da ke gabacin Qalqiliya, da kuma Beithlaham.

Rahotanni daga majiyar Palasdinawa ta tabbatar da cewa sojojin mamayar sun kuma kai wasu hare-haren a sansanin 'yan gudun hijira na garin Salim da ke gabacin Nablus da kuma yankin Saddul-Fahas.

A wani labarin daga Palasdinu, 'yan mamaya na ci gaba da tsare kwamandan kungiyar gwgawarmaya ta Burkan, Ashraf Na'alu wanda ya kai hari akan yahudawa 'yan share wuri zauna

Na'aluh ya kai harin ne a kusa da sansanin yahudawa 'yan share wuri zauna na Ar'el a arewacin Kudus, wanda ya yi sanadiyyar halakar biyu daga cikinsu