Dec 14, 2018 04:22 UTC
  • An Cimma Yarjejeniya Tsakanin 'Yan Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankunan dake fama da rikici a Yemen, bayan tattaunawar neman zaman lafiya data gudana a Swiden tsakanin bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen.

Yarjejeniyar dai ta tanadi masu dauke da makamai daga bangarorin dake rikici a kasar su fice daga yankin Hodeida wanda ya kunshi tashar ruwa wanda ta nan ne ake shigo da mafi yawan kayan agaji dana abinci.

Wannan yarjejeniyar dai zata bada damar taimakawa milyoyin 'yan kasar  ta Yemen dake cikin tsaka mai wuya a yakin da aka kwashe sama da shekara hudu anayi a wannan kasa inji sakatare janar na MDD, Antonio Guteres.

A watan Janairu na shekara mai zuwa ne ake sa ran bangarorin biyu zasu sake yin wani zama domin tattauna domin mangance rikicin ta hanyar siyasa.

Kafin nan dai MDD, zata aike da jami'anta talatin domin sanya ido a birnin na Hodeida.

Tags