MDD Na Kokarin Kare Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki A Yemen
Mai magana da yawun babban magatakardar MDD ne ya tabbatar da cewa Majalisar tana iya kokarinta domin ganin ana ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar yakin
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato Farhan Haqq yana cewa; Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya akan kasar Yemen, Martin Griffiths zai ziyarci kasar Yemen domin tattaunawa da dukkanin bangarorin kasar
Farhan Haqa ya kara da cewa; Idan Griffiths ya kammala ziyararsa a Yemen, zai kuma ziyarci kasar Yemen domin ganawa da Abdu Rabbuhu Mansur Hadi.
An kuma tsara cewa bangarorin biyu masu fada da juna a kasar Yemen za su yi wata ganawa da tattaunawa a kasar Kuwaiti
A can kasar Yemen din dai an zargi kawancen da Saudiyya take jagoranta da keta yarjejeniyar tsagaiwa wutar yaki a yankin Hudaidah
Bangarorin kasar Yemen sun cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ne a wata tattaunawa da su ka yi a kasar Sweeden a watan Disamba da ya shude