Jan 05, 2019 15:42 UTC
  • Wakilin MDD Kan Rikicin Yemen Ya Isa Birnin Sanaa

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin kasar Yemen, Martin Griffiths, ya isa Sanaa, babban birnin kasar Yemen inda zai tattaunawa da 'yan houtsis a wani mataki na kara karfafa wa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a birnin Hodeida wanda ya kunshi tashar jiragen ruwa.

Haka kuma Mista, Griffiths, zai isa a birnin Riyad na kasar Saudiyya, inda zai gana da shugaban kasar ta Yemen mai gudun hijira da kuma wasu manyan jami'ai.

MDD, dai na fatan hada dukkan bangarorin kasar ta Yemen kafin nan da karshen watan nan na Janairu domin waiwaye akan inda aka kwana kan yarjejeniyar da aka a watan Disamba da ya wuce a Sweden.

Yarjejeniyar da bangarorin suka cimma a Sweden ta tanadi shirin tsagaita wuta da ya fara aiki a ranar 18 ga watan Disamban da ya shude a birnin Hodeida dake yammacin kasar da kuma janyewar masu dauke da makamai a birnin da ya kunshi tashar ruwa wanda ta nan ne ake shigar da galibin tallafin kayen abinci da kuma na jin-kai.

A cewra MDD, an samu dan sukuni biyo yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a yankin na Hodeida, saidai ana ci gaba da samun bayyanai na zargin juna da keta yarjejeniyar daga bangarorin dake rikicin.

A wata wasika data aikewa MDD, gwamnatin Yemen mai murabun ta zargi 'yan Houtsis da keta sabawa yarjejeniyar, a yayin da su kuwa 'yan Houstis ke zargin jiragen saman kawancen da Saudiyya ke jagoranta da yin shawagi kasa-kasa a birnin da suke rike da.

A mako mai zuwa ne ake sa ran wakilin MDD kan rikicin kasar ta Yemen, Martin Griffiths zai gabatar da rahotonsa ga kwamitin tsaro na MDD.

Rikicin Yemen dai ya jefa kasar cikin bala'i mafi muni a duniya, inda mutane kimanin Miliyan ashirin ke fama da matsalar karamcin abinci a cewar MDD, a yayin da kuma rikicin da ya fara a shekara 2015 ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 10,000. 

Tags