Jan 12, 2019 13:53 UTC
  • An Gwabza Fada Tsakanin Bangarorin Dake Rikici A Yemen

Rahotanni daga Yemen na cewa wani fada ya sake barkewa da sanyin safiyar yau Asabar a yankin Hodeida tsakanin bangarorin dake rikici a kasar, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma a tsakiyar watan Disamba da ya gabata.

Bayanai sun nuna cewa an yi ta harbe harbe da manyan makamai a kudancin birnin mai matukar mahimmanci wanda yake da matukar mahimmanci wajen shigar da kayan agaji a wannan kasa da yakin kusan shekara hudu ya daidaita.

Majiyoyi sun ce an samu saukin lamarin daga bisani.

Birnin Hodeida dake karkashin ikon 'yan Houtsis, ya kasance tsawan wattani yankin da aka fi gwabza fada tsakanin bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen.

A watan Disamba da ya shude ne bangarorin dake rikici a kasar suka cimma yarjejeniyar tsagaita buda wuta a shiga tsakanin Majalisar Dinkin Duniya a tattaunawar data gudana a kasar Sweden.

A cewar MDD, bangarorin na kiyaye yarjejeniyar, saidai yadda bangarorin biyu ke kara jibge dakarunsu a yankin sabanin yadda yarjejeniyar da aka cimma tayi tanadi, na daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta.

Yakin da Saudiyya ke jagoranta tun cikin shekara 2015 a kasar ta Yemen, ya dai yi sanadin mutuwar kimanin mutum 10,000 tare da jefa kasar cikin bala'i mafi muni a duniya a cewar MDD, a yayin da wasu kungiyoyin ke cewa adadin ma ya haura hakan.

Tags