Kungiyar Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Kasar Chadi
(last modified Mon, 21 Jan 2019 19:15:32 GMT )
Jan 21, 2019 19:15 UTC
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Kasar Chadi

Kungiyar gwagwarmayar musulinci ta Palastinu Hamas ta yi Allah wadai da kokarin da kasar Chadi ke yi na maida alakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila

Kafar watsa labaran Palastinu ta nakalto Isam Da'alis jigo a kungiyar Hamas na cewa matakin da gwamnatin kasar Tchadi ta dauka na dawo da alakar diplomasiyarta da haramtacciyar kasar Isra'ila cin mutunci ne ga al'ummar Palastinu da kuma karfafa sahayunawa na tsananta aiwatar da ta'addanci a kan al'ummar Palastinu.

A yayin da yake nuna takaicinsa kan mumunan sakamakon da zai biyu baya na maido da alakar kasar chadi da haramtacciyar kasar Isra'ila, Isam Da'alis ya bukaci hukumomin birnin N'Djamena da su canza ra'ayi kan wannan mataki da suka dauka, sannan kuma su nuna goyon bayansu da kungiyoyin gwagwarmaya na Palastinu.

A jiya Lahadi ne Piraministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shiga  N'Djamena fadar milkin kasar chadi, inda ya gana da Shugaban kasar Idris Deby.

A yayin ganawar, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewar kasar sa da Chadi sun sake kulla sabuwar dangantakar diflomasiya bayan katse ta da suka yi a shekarar 1972.