Burtaniya Zata Rage Yawan Sojojinta A Kasar Siriya
Ministan tsaron kasar Burtaniya ya bada sanarwan cewa gwamnatinsa zata janye rabin jiragen yakin kasar wadanda suka aikin abinda ya kira zaman lafiya a kasar Siriya zuwa gida.
Jaridar "Daily Mail" ta birnin Londan ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Talata, ya kuam kara da cewa jiragen yakin na kasar Burtaniya samfurin Tornador zasu dawo gida akafin karshen wannan watan Janeru da muke ciki.
Shekaru 7 da suka gabata kenan, kasar Britania ta shigo da jiragen yakinta cikin kasar Siriya ba tare da izinin gwamnatin kasar ba, da sunan yaki da kungiyar Daesh karkashin jagoran Amurka a kasar ta Siriya.
Amma bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwa a ranar 19 ga watan Decemban da ya wuce kan cewa zai janye sojojin kasarsa daga kasar Siriya , ita ma kasar Britania ta kuduri anniyar janye rabin jirage yakinta da suke kasar ta Siriya.