Majalisar Wakilan Amurka Ta Amince Da Wani Kuduri Na Takurawa Siriya
(last modified Wed, 23 Jan 2019 07:09:41 GMT )
Jan 23, 2019 07:09 UTC
  • Majalisar Wakilan Amurka Ta Amince Da Wani Kuduri Na Takurawa Siriya

Majalisar wakilai a kasar Amurka ta amince da wani kuduri wanda zai sa gwamnatin shugaban Trump ta kara kakabawa gwamnatin kasar Siriya takunkuman tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labaran Spotnik ya bayyana cewa majalisar ta amince da kudurin ne bayan da komitin al-amuran kasashen waje na majalisar ya kammala tsari hsirin a jiya Talata.

Kudurin zai bawa gwamnatin Amurka damar kakabawa wasu daddaikun mutane a gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad da kuma wasu kamfanonin kasar ta Siriya takunkumai, wadanda zasu hada da na hana gwamnatin kasar siriya amfani da tsarin musayar kudade tsakanin bankuna na kasa da kasa SWIF, hana kamfanonin Amurka wadanda suka hada da na kirar jiragen sama, ko sassan jiragen sama hulda da gwamnatin kasar Siriya. 

Manufar wannan takunkumin dai inji rahoton shi ne take hakkin bil'adama wanda gwamnatin shugaba Bashar Al-asad take yi a kasar Siriya.

Bayan da kasashen yamma sun kasa kifar da gwamnatin shugaba Bashar Al-asad ta hannun yan ta'adda a cikin shekaru 7 da suka gabata , a halin yanzu sun bullo da sunan kare hakkin bil'adama don takurawa gwamnatin kasar ta Siriya.

Kafin haka kungiyar tarayyar Turai ma ta shelantar takunkumin tattalin arziki kan mutane 11 da kuma kamfanoni 5 a kasar ta Siriya su ma da suna take hakkin bil'adama.