Feb 08, 2019 05:20 UTC
  • Bangarorin Dake Rikici A Yemen Na Tattaunawa A Jodan

Bangarorin dake rikici a kasar Yemen na wata tattaunawa a birnin Amman na Jodan, kan musayar fursunoni a tsakaninsu.

Tattaunawar dake gudana a shiga tsakanin Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross, na da manufar cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu kan yadda zasu yi musayar fursunoni.

An dai shirya bangarorin biyu zasuyi musayar fursunoni 15,000 a tsakaninsu, saidai bayanai sun ce har yanzu akwai tazara mai yawa domin cimma matsaya tsakanin wakilian 'yan neman sauyi na Houtsis da kuma na gwamnatin Yemen dake samun goyan bayan Saudiyya.

Hakan dai a cewar majiyoyi zai iya sanya a kwashe watanni da dama ana tattaunawar, duba da jan aikin dake gaba na tantance sunayen mutum 15,000.

Masu shiga tsakanin tattaunawar sun ce sun kwashe sama da wata biyu suna aikin, amma matsalar shi ne basu kai ga gano wasu dubban mutane dake cikin jerin sunayen wadanda ake son musayar dasu ba, wanda a cewarsu kilah wasu mayaka ne wadanda suka ko sun mutu, ko kuma sojoji da ko aka sallama, ko kuma suka ma tsere.

Daga bangaren 'yan Houstis sun ce kawo yanzu kashi 10% ne na mutanensu aka kai ga tantancewa, wanda a cewarta akwai sunaye da dama dake sake bayyana a cikin jerin sunayen.

MDD, da kungiyar ta Red Cross, na fatan bangarorin biyu sun cimma matsaya cikin sauri, domin bada damar kaiwa ga tattaunawar zaman lafiya mai daurewa a kasar ta Yemen.

Tags