Feb 16, 2019 11:02 UTC
  • Sojojin Isra'ila Sun kashe Falastinawa 2 A Yankin Zirin Gaza

A ci gaba da gangamin neman hakkin komawar Falastinawa 'yan gudun hijira a Gaza, sojojin Isra'ila sun kashe Falastinawa tare da jikkata wasu.

Shafin yada labarai na Palastine ya bayar da rahoton cewa, Falastina biyu suka yi shahada a jiya a Juma'a, a gangamin da ake gudanarwa a kowace Juma'a a yankin Zirin gaza, domin jaddada matsayin al'ummar Palastine kan hakkin da dukkanin falastinawa da Isra'ila ta kora daga kasarsu suke da shi na dawowa kasarsu ta asali.

Bayanin ya ce dukkanin falastianwan da suka shahada a jiya matasa ne, kamar yadda kuma a jiya ma sojojin Isra'ila sun harbe wata yarinya bafalastiniya har lahira a yankin gabar yama da kogin Jordan.

Haka nan kuam wasu rahotanni sun tabbatar da cewa ajiya jami'an tsaron yahudawan sahyuniya sun kame adadi mai na matasan falastinawa a cikin yankunan da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Tags