Yemen : Yerjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Soma Aiki
-
Da misalin karfe 12 na daren lahadin nan ne yerjejeniyar ta soma aiki. (hoto © ISNA)
A kasar Yemen, a cikin daren jiya ne yarjejeniyar tsagaita wuta dake samun goyon bayan majalisar dinkin duniya ta soma aiki.
Tsagaita wutar na zuwa ne gabanin tattaunawar zaman lafiya da za a yi ranar 18 ga wata a Koweit tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Houthi.
MDD, ta bukaci masu rikici a kasar ta Yemen dasu mutunta yerjejeniya wace ake fatan zata kawo karshen yakin da yayi sanadin mutuwar mutane fiye da 6,000.
Wata sanarwa da mai shiga tsakani na MDD a rikicin kasar, Ismail Ould Cheikh Ahmed ya fitar gabanin tsagaita wuta ta ce wannan babban ci gaba ne a matakin dawo da zamen lafiya, tare da bada damar isar da kayan agaji ga dubban al'umma wannan kasa da suka tagaiyara sakamakon farmakin ba -gaira-ba dalili da Saudiyya ke jagoranta yau sama da shekara guda.