Shahadar Wani Bapalastine a Hanun Jami'an tsaron HKI
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3883-shahadar_wani_bapalastine_a_hanun_jami'an_tsaron_hki
Jami'an tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila sun bindige wani Bapalastine har Lahira
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 14, 2016 11:07 UTC
  • Shahadar Wani Bapalastine a Hanun Jami'an tsaron HKI

Jami'an tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila sun bindige wani Bapalastine har Lahira

Kamfanin dillancin labaran Palastinu Sama ya habarta cewa A yau Alkhamis Dakarun tsaron HKI sun halbe wani matashin Palastinawa a kofar shigar sansanin Al'arub na arewacin Alkhalil dake gabar tekun Jodan, lamarin da ya yi sanadiyar shahadarsa.

A nasu bangare Dakarun tsaron HKI sun bayyana cewa Bapalastinan ya kai harin ne a kansu su kuma suka bindige shi.

A bangare guda Dakarun tsaron HKI sun kai hari a yankuna daban daban na gabar tekun jodan da kuma Baitul-Makdis inda suka yi awan gaba da Palastinawa 10 daga ciki har da kananen yara guda biyu.

Har ila yau a yau din Sojojin HKI sun kai farmaki kan wani Bapastine Dan canji tare da rike masa kudadensa, lamarin da ya janyo barkewar rikici tsakanin su da Palastinawan.

Tun daga farkon watan Oktoban shekarar 2015 zuwa yanzu,yankuna daban daban na Palastiwan ke fuskantar rikici da kuma hare-hare kan Al'ummar Palastinu daga Yahudawa 'yan kama guri zauna da kuma Sojojin HKI din, lamarin da ya janyo Intifadar Qudus, daga wancan lokacin zuwa yanzu, Sojojin HKI sun kashe Palastinawa 212 tare kuma da jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu.

Gwagwarmayar Palastinawa a matsayin mayar da martani ya zuwa yanzu ya hallaka Yahudawan akalla 34.