Tattaunawa Sulhu Kan Rikicin Kasar Yemen A Koweit
Apr 18, 2016 04:38 UTC
-
tattaunawa sulhu kan rikicin Yemen a Geneva (hoto rumbun ajiya)
Yau Litinin ake fara tattaunawa neman sulhu kan rikicin kasar Yemen a shiga tsakanin majalisar dinkin duniya a kasar Koweit.
Tattaunawar dai zata kasance tsakanin wakilan kungiyar 'yan gwagwarmaya neman sauyi ta Ansarallah da ake kira 'yan Houtsis da kuma gwamnatin kasar mai murabus domin kawo karshen zubar da jini da aka shafe watanni 13 ana yi a wannan kasa.
Saidai kafin hakan mai shiga tsakani a rikicin kasar, Ismaïl Ould Cheikh Ahmed ya bayyanawa kwamitin tsaro na MDD matukar damuwar sa dangane da tabarbarewar yanayin da ake ciki a kasar ta Yemen.
Hakan dai na nufin har yanzu akwai babban sabani tsakanin bangarorin biyu.
Tags