MDD ta bukaci da tattaunawar sulhun kasar Yemen cikin gaggawa
Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci bangarorin da ake fada a kasar Yemen su fata tattauna ba tare da bata lokaci ba
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Stephane Dujarric kakakin Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya a jiya Talata na cewa muna kyatata fatan cewa magabatan Saudiya da na Alhusi bisa shiga tsakanin Isma'il wul Sheikh Ahmad wakilin Majalisar dinkin Duniya za su fara tattauwar sulhun ba tare da bata lokaci ba.
A cewar Dujjaric tun daga ranar 11 ga watan wanan na Avrilu da muke ciki ne bangarorin biyu suka amince da tsagaita wuta tare da yin alkawarin za su hau kan tebirin shawara a kasar Kuweit domin magance sabanin dake tsakanin su. sai dai babban abin damuwa a nan shi ne har yanzu ba a fara tattauwar ba, don haka MDD take kira da babban murya ga bangarorin biyu su fara tattaunawar.
Bisa rahoton na MDD daga lokacin da masarautar Ali-sa'oud ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen zuwa yanzu, sama da Mutane dubu 6 da 400 ne suka yi shahada daga cikin su har da Mata da kananen Yara.