Za'a Fara Taron Sulhu Na Kasar Yemen A Kasar Kuwait
Majiyar Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa a gobe Alhamis ne za'a fara taron
Majiyar Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa a gobe Alhamis ne za'a fara taron sulhuntawa na kasar Yemen a kasar Kuwai. Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin Kuwaita ya nakalto Stivin Dujorik wakilin majalisar dinkin duniya a rikicin kasar ta yemen yana fadar haka a yau Laraba.
Labarin ya kara da cewa waikin kungiyar yan Huthi da kuma kawayensu sun isa birnin Kuwait don halattan taron wanada za'a fara a gobe.
Tun fiye da shekara guda kenan gwamnatin kasar Saudia da kawayenta suke luguden wuta kan yankunan daban daban na kasara Yemen da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Hadi Mansur kan kujerar shugabancin kasar.,
Dubban mutanen ne mafi yawansu mata da yara suka rasa rayukansu tun lokacin fara yankin. Sannan wasu miliyoyi kuma suka yi gudun hijira daga kasar. A halin yanzu dai mafi yawan kasar Yemen tana hannun sojojin kasar da kuma mayakan huthi.