Za'a Fara Tattaunawar Sulhu Kan Rikicin Yemen Yau A Kasar Kuwait
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4177-za'a_fara_tattaunawar_sulhu_kan_rikicin_yemen_yau_a_kasar_kuwait
Yau Al'hamis wakilai daga bangarorin dake rikici a kasar Yemen ke fara wani zamen tattaunawa kan samar da zamen lafiya a wannan kasa a shiga tsakani na MDD a kasar Koweit.
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 21, 2016 01:20 UTC
  • Za'a Fara Tattaunawar Sulhu Kan Rikicin Yemen Yau A Kasar Kuwait

Yau Al'hamis wakilai daga bangarorin dake rikici a kasar Yemen ke fara wani zamen tattaunawa kan samar da zamen lafiya a wannan kasa a shiga tsakani na MDD a kasar Koweit.

Tuni dai 'yan gwagwarmaya na neman sauyi na Houtsi a kasar ta Yemen suka bayyana aniyar su ta shiga tattaunawar da nifin kawo karshen zubar da jini da aka kwashe wattanni 13 ana yi a kasar ta Yemen.

A cikin wasikar da aka aika a jajibiri zuwa ga manzon MDD dake kasar Yemen, Ismail Ould Cheik Ahmed, 'yan Houthi da magoya bayan tsohon shugaban kasa sun tabbatar cewa wakilansu za su isa kasar Koweit domin halatar taron shawarwari.

Taron na zuwa a daidai lokacin da dukkan bangarorin biyu ke sargin junan su da keta yerjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tun a ranar 11 ga wata da nifin bada damar kaiwa ya taro sharwarwarin samar da zamen lafiya