Akwai Ci Gaba A Tattaunawar Sulhun Yemen
-
Mai shiga tsakani na mdd a rikicin kasar Yemen, Ismail Ould Cheikh Ahmed
Rahotanni daga Koweit na cewa ana samun fahimtar juna a tattaunawar farko ta gaba da gaba da akeyi tsakanin masu rikici a kasar Yemen a shiga satkanin MDD.
A jiya Asabar bangarorin biyu sunyi tattaunawar keke-da-keke wace a yayin ta suka tabo batutuwa da dama da suke da sabani a kai.
Mai shiga tsakani a rikicin kasar Ismail Ould Cheikh Ahmed ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa akwai ci gaba da fahimtar juna sosai a tattaunar da aka fara tun ranar 21 ga watan jiya, wanda a cewar sa abun yabawa ne, duk da cewa babu tabas.
Wanan dai shi ne karo farko da bangaren 'yan gwagwarmaya neman sauyi na Houtsis dana gwamnatin Yemen suka tattaunawa ta keke-da- keke.
Ana dai yin tattaunawar ce domin kawo karshen zubar da jinin da aka shafe sama da shekara ana yi a wannan kasa ta Yemen.