Sojojin Amurka Na Yakar Al'Qaida A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4870-sojojin_amurka_na_yakar_al'qaida_a_yemen
Amurka ta tabbatar da cewa wasu sojojin ta sun isa kasar Yemen domin taimakawa kawacen da Saudiyya ke jagoranta wajen yaki da 'yan ta'ada Al'Qaida a yankin Moukalla dake kudu maso gabashin kasar ta Yemen.
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 07, 2016 01:23 UTC
  • wasu sojojin Amurka
    wasu sojojin Amurka

Amurka ta tabbatar da cewa wasu sojojin ta sun isa kasar Yemen domin taimakawa kawacen da Saudiyya ke jagoranta wajen yaki da 'yan ta'ada Al'Qaida a yankin Moukalla dake kudu maso gabashin kasar ta Yemen.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar jiya juma'a ta ce, tun daga 23 ga watan Afrilu daya gabata Amurkar ta kai hare-hare ta sama daban-daban har guda hudu kan 'yan Al'Qaida tare da hallaka 10 daga cikin su a kasar ta Yemen.

Wannan dai shi ne karo farko da ma'aikatar Pantagone ta sanar da sake komawar sojojin Amurka a Yemen, tun bayan ficewarsu a watan Maris daya gabata.

kungiyar Al'Qida dai tayi amfani na amfani da rikicin da kasar Yemen ta tsunduma yau sama da shekara guda domin fadada ayyukan ta a wasu sassan kasar ta Yemen musamen a Yankin Moukalla.