An kame Shugaban Kungiyar Saleka a Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4876-an_kame_shugaban_kungiyar_saleka_a_kamaru
Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da kame Shugaban Kungiyar 'yan tawayen Saleka na kasar Afikra ta tsakiya a kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:14+00:00 )
May 07, 2016 09:51 UTC
  • An kame Shugaban Kungiyar Saleka a Kamaru

Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da kame Shugaban Kungiyar 'yan tawayen Saleka na kasar Afikra ta tsakiya a kasar.

Majiyar ta sanar da cewa A ranar 29 ga watan Avrilun da ya gabata aka cabke Mahamat Aboubakar Shugaban kungiyar Saleka na Afirka ta tsakiya a yankin Ngaoui dake kan iyakaokin kasar biyu, wannan na zuwa ne bayan wasu bayyanan sirri da mazauna yankin suka baiwa jami'an tsaron Gandarma.

A ranar 24 ga watan Avrilun da ya gabata ne mista Mahamat ya tsere cikin kasar ta Kamaru bayan wani gumurzu tsakanin mayakan sa da na Anti-balaka.

Yanzu haka dai ana tsare da Shugaban kungiyar ta Saleka a gidan yarin Yawunde babban birnin kasar kamaru.