Yemen : IS Ta Kashe 'Yan Sanda Sabbin Dauka 25
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5218-yemen_is_ta_kashe_'yan_sanda_sabbin_dauka_25
Rahotanni daga kasar Yemen na cewa 'yan sanda sabbin dauka 25 ne suka rasa rayukan su biyo bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wata cibiyar horaswa a kudu maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 15, 2016 06:29 UTC
  • Yemen : IS Ta Kashe 'Yan Sanda Sabbin Dauka 25

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa 'yan sanda sabbin dauka 25 ne suka rasa rayukan su biyo bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wata cibiyar horaswa a kudu maso gabashin kasar.

tuni kungiyar 'yan ta'adan IS ta dauki alhakin kai harin.

ko baya ga wadanda suka rasun an samu wasu mutane 25 da suka raunana a cewar rahotanni.

ko a kwanaki uku da suka gabata ma kungiyar IS ta kai wani hari makamancin wannan wanda yayi sanadin mutuwar sojojin kasar ta Yemen guda goma a yankin na Moukalla.