Dakarun Iraki Sun Hallaka Wasu Gwamnonin Kungiyar Da'esh Biyu A Kasar
Rahotanni daga kasar Iraki sun bayyana cewar dakarun kasar sun sami nasarar hallaka wasu gwamnoni guda biyu da kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh ta nada a yankunan da suka kama a wasu hare-hare da suka kaddamar.
Tashar talabijin din Al-Sumaria ta kasar Irakin ta bayyana cewa a wani hari ta sama da sojojin Irakin suka kaddamar sun sami nasarar hallaka Muhammad Al-Waziri, gwamnan Kungiyar Da'esh din a lardin Kirkuk da ke hannun 'yan ta'addan, baya ga wasu 'yan ta'adda 30 da su ma suka hallaka.
Har ila yau rahoton ya kara da cewa sojojin na Iraki a wani harin kuma na daban da suka kaddamar sun sami nasarar hallaka wani gwamnan na Da'esh mai suna Abu Hamza da wasu 'yan ta'adda su biyar a lardin Anbar.
Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai sojojin Irakin da suke samun goyon bayan dakarun sa kai na kasar suna ci gaba da samun nasarori a kan 'yan ta'addan na Da'esh da kwace yankunan da suke rike da su.