Harin Dakarun HKI kan Manonan Palastinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6241-harin_dakarun_hki_kan_manonan_palastinawa
Sojojin Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da karya yarjejjeniyar tsagaita inda suka kai hari kan manoma da makiyayan Palastinawa a yankin Zirin Gaza.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 04, 2016 13:53 UTC
  • Harin Dakarun HKI kan Manonan Palastinawa

Sojojin Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da karya yarjejjeniyar tsagaita inda suka kai hari kan manoma da makiyayan Palastinawa a yankin Zirin Gaza.

Tasha telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a yau Assabar Sojojin HKI sun buda wuta kan manoma da makiyan Palastinawa a garin Khan Yunus dake gudancin zirin Gaza, harin da ya tilasta musu barin yankin, saidai har yanzu babu wani cikekken bayyani kan hasarar da wannan hari ya janyo.

Duk wani hari da za aka kai zirin Gaza, karya yarjejjeniyar sulhun da aka cimma tsakanin kungiyar gwagwarmayar Palastinawa da magabatan Haramcecciyar kasar Isra'ila na watan Augustan shekarar 2014, bayan yakin kwanaki 50 na shekarar 2014 bisa tsiga tsakanin kasar Masar.

Idan ba a manta ba dai cikin wannan kwanaki 50 da Dakarun HKI suka yi suna ruwan bama-bamai kan Al'ummar Zirin Gaza kimanin Palastinawa 2300 ne suka yi shahada yayin da wasu dubai na daban suka jikkata.

A harin kare kai da matasan Palastinawa ke kaiwa kan Dakarun tsaron HKI , A yau Assabar Matasan Palastinawan sun jikkata kwamondoji sjin HKI biyu a gefen tekun jodan da kuma gefen Baitul-Makdis.