Yemen : An Cimma Yarjejeniyar Sakin Yara Fursunoni
Jun 06, 2016 06:11 UTC
Ana ci gaba da tattaunawar neman sulhu dake gudana a kasar Kowait, bangarorin dake rikici a kasar Yemen sun cimma yerjejeniyar sakin yara fursunoni da suke tsareda ba tare wata-wata ba.
Wakilin mdd kan rikicin kasar, Ismaïl Ould Cheikh Ahmed ne ya sanar da hakan, a wannan Litinin.
A cewar babban jami'in idan dai har bangarorin biyu suka mutunta wannan yarjejeniyar, to zai zamo wani babban ci gaba da aka samu a tattaunar neman sulhu da ake fatan cimmawa tsakanin masu gwagwarmaya neman sauyi na Houtsi da kuma wakilan gwamnatin kasar mai murabus.
Tags