Kuwaiti: Tattaunawa Akan Yemen Tana Ci gaba.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6958-kuwaiti_tattaunawa_akan_yemen_tana_ci_gaba.
Ma'aiktar harkokinWajen Kasar Kuwaiti Ta ce; Ana Samun ci gaba A tattaunawar mutanen Yemen.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 19, 2016 14:49 UTC
  • Kuwaiti: Tattaunawa Akan Yemen Tana Ci gaba.

Ma'aiktar harkokinWajen Kasar Kuwaiti Ta ce; Ana Samun ci gaba A tattaunawar mutanen Yemen.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Kuwaiti da ta ke daukar bakuncin tattaunawar bangarorin kasar Yemen masu sabani,ta ce; ana samun cin gaba a tattaunawar da ake yi.

Mataimakin ministan harkokin wajen Kuwaitin Khalid Jarullah ya ce; Bangaren Abdulhadi Mansur- da ke da goyon bayan Saudiyya- da kuma bangaren Ansarullah, suna musayar ra'ayi.

Khalid Jarallah ya ci gaba da cewa; Kasarsa ba ta tsoma baki a cikin tattaunawar da bangarorin na kasar Yemen su ke yi.

Fiye da wata daya kenan dai da bangarorin na Yemen da su ke yaki da juna su ka bude tattaunawa a kasar Kuwaiti da zummar samun mafita.

Saudiyya da kawayenta larabawan tekun pasha sun shelanta yaki akan kasar Yemen mai makwabtaka da ita.

kawo ya zuwa yanzu dai dubban mutane ne su ka mutu, yayin da wasu dubban su ka jikkata.