MDD:Rabin Mutanan Yemen suna cikin Yunwa
Kungiyar Abinci da aikin Noma ta MDD ta ce Mutanan jahohi 19 daga cikin Jahohi 22 na kasar Yemen na fuskantar matsalar karamcin Abinci
A cikin wani rahoto da ta fitar jiya Kungiyar ta FAO ta ce a halin da ake ciki sama da kashi 50% na Mutanan Kasar Yemen musaman mazauna jahohi19 na cikin mawuyacin hali na karamcin abinci, kuma kashi 70% na Al'ummar kasar sai sun sha matsananciyar wahala kafin su samu abinci da za su ci.
A cewar Salahu din Alhaji Hasan wakilin kungiyar FAO a Yemen, ci gaba da rikci da kuma yadda 'yan gudun hijra ke karuwa a yankuna daban daban na kasar ya janyo babbar asara ga manoma kasar kuma tanadin da manoma suka yi ya kawo karshe. domin haka wajibi kungiyoyin kasa da kasa su taimaka wajen ceto sama da Mutanan kasar miliyan biyu daga halaka.
A nata bangare Bettina Lüscher mai magana da yawun hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da abinci, wadda ta ce halin da kasar ta Yemen ke ciki na bukatar agajin gaggawa.
Rahoton hukumar ya ce an samu karin kashi 15 cikin 100 na mutanen da suka shiga matsalar yunwa, inda aka kwatanta daga watan Yuni na shekarar da ta gabata ta 2015.
A halin da aka ciki Fiye da 'yan Yemen milyan biyu suka tsere daga gidajensu samakaon rikicin da kasar ta samu kanta a ciki.