Halakar Sojojin Hayar Saudiyya A Birnin Sana'a Fadar Mulkin Kasar Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7846-halakar_sojojin_hayar_saudiyya_a_birnin_sana'a_fadar_mulkin_kasar_yamen
Sojojin gwamnatin Yamen sun kai farmaki da makamai masu linzami kan sansanin sojojin hayar masarautar Saudiyya a birnin Sana'a fadar mulkin kasar ta Yamen, inda suka kashe sojojin haya masu yawa.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 09, 2016 05:46 UTC
  • Halakar Sojojin Hayar Saudiyya A Birnin Sana'a Fadar Mulkin Kasar Yamen

Sojojin gwamnatin Yamen sun kai farmaki da makamai masu linzami kan sansanin sojojin hayar masarautar Saudiyya a birnin Sana'a fadar mulkin kasar ta Yamen, inda suka kashe sojojin haya masu yawa.

Tashar talabijin ta Masirah a yau Asabar ta watsa rahoton cewa: Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa- kai masu rufa musu baya sun harba makamai masu linzami kan sansanin sojojin hayar masarautar Saudiyya da ke yankin Fardhat -Nihim a siyar arewa maso gabashin birnin Sana'a fadar mulkin kasar ta Yamen, inda suka kashe adadi masu yawa tare da jikkata wasu na daban.

Kakakin rundunar sojin gwamnatin Yamen Sharq Luqman ya bayyana cewa: Harin yana matsayin daukan fansa ce kan matakin rashin mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin gwamnatin Yamen da Masarautar Saudiyya, inda jiragen saman yakin Saudiyya ke ci gaba da yin luguden wuta kan yankunan kasar ta Yamen.