Dakarun Yemen Sun Kakkabo Jirgin Leken asirin Saudiya a Birnin Sana'a
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7918-dakarun_yemen_sun_kakkabo_jirgin_leken_asirin_saudiya_a_birnin_sana'a
Dakarun sojin Kasar Yemen sun tarwatsa Jirgin Leken asirin kasar Saudiya a sararin smaniyar birnin Sana'a fadar milkin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 11, 2016 01:18 UTC
  • Dakarun Yemen Sun Kakkabo Jirgin Leken asirin Saudiya a Birnin Sana'a

Dakarun sojin Kasar Yemen sun tarwatsa Jirgin Leken asirin kasar Saudiya a sararin smaniyar birnin Sana'a fadar milkin kasar

Rahotani daga kasar Yemen sun tabbatar da cewa a jiya Lahadi Dakarun tsaron sararin samaniyar kasar sun tarwatsa wani Jirgin Leken asiri na masaurautar Ali sa'oud a sararin samaniyar birnin Sana'a.

Wani Jami'in tsaron kasar Yemen din da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa manema Labarai cewa Dakarun tsaron sararin samaniyar kasar sun samu nasarar gano jirgin ne a yayin da yake shawagi a sararin samaniyar yanki na 9 na birnin Sana'a fadar milkin kasar

Jami'in ya kasa da cewa Jirgin Leken Asirin na Saudiya na cikin aikinsa, inda ya fara daukan poto na barikokin soja da na Dakarun sa kai na kungiyar Ansarul... sai Dakarun tsaron sararin samaniyar kasar suka gano shi kuma suka tarwatsa shi.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da Dakarun tsaron Yemen din ke tarwatsa Jiragin leken asiri na Masarautar Ali sa'oud, a baya ma Dakarun tsaron sararin samaniyar kasar Yemen din sun kakkabo jiragen lelen asirin masarautar Ali sa'oud da dama a yankuna daban daban na kasar