An Halaka Sojojin Mamaya 179 A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8242-an_halaka_sojojin_mamaya_179_a_yemen
Sojojin kasar Yemen tare da sojojin sa kai na kabilun larabawan kasar sun harba makami mai linzami a kan wani dandazon sojojin mamaya karkashin jagorancin Saudiyya a kudancin Ta'iz, inda da dama daga cikinsu suka halaka.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 17, 2016 06:50 UTC
  • An Halaka Sojojin Mamaya 179 A Yemen

Sojojin kasar Yemen tare da sojojin sa kai na kabilun larabawan kasar sun harba makami mai linzami a kan wani dandazon sojojin mamaya karkashin jagorancin Saudiyya a kudancin Ta'iz, inda da dama daga cikinsu suka halaka.

Shafin watsa labarai na ra'yul Yaum ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga rundunar sojin kasar Yemen cewa, an yi amfani da makami mai linzami na ballistic ne wajen mayar da martani kan sojojin na mamaya, wadanda suka hada da sojojin kasar Saudiyya da kuma sauran sojojin hayar da ta dauka daga kasashe daban-daban domin taya ta yaki kan al'ummar Yemen.

Tashar talabijin ta Almasira ta kasar Yemen ta bayar da rahoto a yau Lahadi cewa, harin na dakarun kasar da kuma sojojin sa kai ya zo ne domin mayar da martani a kan 'yan mamaya kan harin da suka kaddamar kan birnin San'a a cikin wannan mako, tare da kashe fararen hula da dama.