Dakarun tsaron yamen sun hallaka sojojin Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8650-dakarun_tsaron_yamen_sun_hallaka_sojojin_saudiya
Sojojin Saudiya da dama ne suka hallaka a harin makami mai lizzami na Dakarun tsaron Yemen a kudu maso yammacin saudiya
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 25, 2016 06:31 UTC
  • Dakarun tsaron yamen sun hallaka sojojin Saudiya

Sojojin Saudiya da dama ne suka hallaka a harin makami mai lizzami na Dakarun tsaron Yemen a kudu maso yammacin saudiya

Tashar Telbiji din Almasira ta kasar Yemen ta Habarta cewa Dakarun tsaron kasar sun halba makamai masu lizzami a sansanin sojin Saudiya dake jihar Jizan, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da kuma jikkata da dama daga cikin Sojojin na Saudiya.

Har ila yau Dakarun na Yemen sun kai wani farmaki a guraren sojojin Saudiyar a yankin Rabou'a dake jihar Asir tare da hallaka biyu daga cikin su.

A jiya Lahadi ma Dakarun na Yemen sun kai wani farmaki a guraren taruwar Sojojin Saudiya a Jihar Jizan tare da hallaka wani adadi daga cikin su.

A bangare Jiragen yakin Saudiyan sun kai hari kan gidajen fararen hula a garin Abas dake Jihar Hijja na Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar rusa gidajen baki daya. ya zuwa yanzu babu wani cikekken bayyani dangane da adadin mutanan da suka yi shahada ko kuma suka jikkata sanadiyar wannan hari.