An hallaka tare da jikkata Sojojin hanyar Saudiya 50 a yemen
Dakarun tsaron Yemen sun halba makami mai lizzami a gurin taruwar Sojojin hanyar saudiya , lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da jikkata kimanin 50 daga cikin su.
Tashar Telbijin din Almasira ta kasar yemen ta nakalto majiyar tsaron kasar a wannan Laraba na cewa Dakarun tsaron Yemen sun halba wani makami mai lizzami wanda aka kera shi a cikin kasar da kuma aka bashi sunan Zilzali na 3 a gurin taruwar Sojojin hayar saudiya dake yanki na 9 a birnin Sana'a , lamarin da ya yi sanadiyar hallaka da jikkata kimanin 50 daga cikin su.
Rahoton ya ce an kai harin ne a yayin da Sojojin hayar Saudiyan ke shirye-shiryen kai hari a yankin Mujawiha.
A matsayin martani na hare-haren wuce gona da irin da kuma ruwan bama-baman da jiragen yakin saudiya ke yi ba dare ba rana a kan fararen hula, Sojoji da Dakarun sa kai na Ansarul...na ci gaba da kai hare-hare na makami mai lizzami kan guraren taruwar sojojin hayar saudiyan a cikin kasar ta Yemen.