Yemen : 'Yan Houthis Sun Kafa Majalisar Koli
'Yan gwagwarmayar neman sauyi na Houthis a Yemen sun kafa wata majalisar koli domin shugabancin kasar.
A sanarwar da suka fitar 'yan Houthis sun ce sun kafa majalisar da hadin gwiwar jam'iyyar CPG ta tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh data kunshi mambobi guda goma.
Babban aikin wannan majalisa a cewar bangarorin biyu, shi ne hada karfi-da-karfe domin kalubalantar duk wata barazana daga kawacen da Saudiyya ke jagoranta.
Hakazalika a cewar sanarwar, wani aikin majalisar shi ne tafiyar da harkokin al'umma ta bangaren siyasa, da soji da tattalin arziki da ma'aikatu da kuma tsaro.
Saidai tuni bangaren gwamnatin Abdul Rabo Mansur hadi mai murabus ta ce ta janye daga tattaunawar sulhu da ake a Kuwait, saboda wannan matakin na 'yan Houthis.