MDD Ta Dakatar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Rikicin Yemen
MDD ta sanar a wannan Asabar a Kowait cewa ta dakatar da tattaunar zamen lafiya ta wani dan lokaci kan rikicin kasar Yemen.
An dai dakatar da tattaunawar da ake yi inji MDD tsakanin 'yan gwagwarmaya na Houtsi da kuma gwamnatin kasar mai murabus har na tsawan wata guda aman za'a komo tattaunawar anan gaba domin kawo karshen yakin daya daidaita wannan kasa ta Yemen.
Mai shiga tsakani na MDD, Ismaïl Ould Cheikh Ahmed, ya shaidawa manema labarai a Kowait cewa bangarorin biyu sun tabbatacin cewa zasu dawo a ci gaba da tattaunawar nan gaba, saidai ba tare bayana inda hakan zata kasance ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Houtsi suka sanar da sunayen membobin majalisar da suka kafa domin jagorancin kasar.
Rikicin kasar Yemen dai ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 6,400 tare da cilastawa wasu miliyan biyu da dari takwas tserewa daga gidajen su.