Ta'addancin Saudiya A Yemen
Kasar Saudiya ta yi ruwan bama-bamai masu guba a wani yanki na birnin Sana'a fadar milkin kasar Yemen
Rahotanni dake fitowa daga kasar Yemen sun tabbatar da cewa a daren jiya Assabar jiragen yakin kawacen saudiya sun ruwan bama-bamai na makamai masu guba a gunduma ta tare da kuma kauyukan dake kewayen da ita na birnin Sana'a fadar milkin kasar, lamarin da ya sanya Al'ummar dake yankin suka wayi gari cikin mawuyacin hali na raunin jiki.
Amfani da makamai masu guba kan Al'ummar Yemen daga kawancen saudiya ya karu a baya bayan nan, duk da cewa a watanin da suka gaba Jiragen yakin kawaucen saudiyar sun yi ta kai hare-hare a wannan yanki,inda wasu ke ganin cewa masarautar Ali sa'oud din ta samu wannan nau'i na makamai masu guba ne daga kasashe aminanta irin su haramcecciyar kasar Isra'ila domin ci gaba da ta'addanci a kasar ta Yemen.
Har ila yau, Jiragen yakin na kawancen Saudiya sun yi ruwan bama-bamai a garin Kataf dake jihar Sa'ada.
A nasu bangare, Dakarun tsaron Yemen tare da na sa kai sun samu nasarar dakile wani ci gaba na mamayar sojojin hayar Saudiya a yankin Malah inda suka hallaka tare da jikkata wani adadi na Sojojin hayar saudiyar.sannan kuma sun yi ruwan makamai masu lizzami a guraren tauwar Sojojin hayar Saudiyar dake ariruwan Alkhuba, Jizan da kuma yankin Sakam na jihar Najran.