-
Iraki: An Kashe 'Yan Da'esh 130 Da Suke Gudu Daga Talla'afar
Aug 30, 2017 02:26Sojojin Peshmarga na Kurdawa ne suka sanar da kashe 'yan Da'esh da suka gudo daga garin Talla'afar.
-
Masar: An Daure Wasu "Yan Adawa 25 Zaman Kurkuku Na Rai Da Dai.
Aug 30, 2017 02:26Kutun da ta daure 'yan adawar ta same su da laifin shiga cikin tashe-tashen hankulan da su ka faru a kasar a 2015
-
Unicef: Fiye Da Yaran Kasar Yemen 1700 Ne Suka Rasa Rayukansu
Aug 30, 2017 02:24Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Yemen ya ce; Daga lokacin da Saudiyya ta fara hari zuwa yanzu, an kashe yara fiye da 1700.
-
Bukatar Fira Ministan Hukumar Palasdinawa Ga Majalisar Dinkin Duniya
Aug 29, 2017 14:27Fira ministan hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarta wajen kawo karshen bakar siyasar zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu.
-
Dakarun Kurdawar Kasar Iraki Sun Kashe 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Fiye Da 130
Aug 29, 2017 14:26Dakarun yankin Kurdawa mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Iraki sun kashe mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish fiye da 130 a kokarin da 'yan ta'addan suke yi na tsallakawa cikin kasar Siriya bayan da aka fatattake su daga garin Tala'afar na Iraki.
-
Adadin Mahajja A Bana Ya Karu Da Kusan Rabin Miliyan
Aug 29, 2017 07:36Mahukuntan kasar saudiyya sun ce adadin mahajjatan bana ya karu da kusan maniyyata rabin miliyan, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
-
Sayyid Nasrallah: 'Yan Da'esh Ba Su Da Wata Mafita Face Mika Kai
Aug 29, 2017 01:10Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da aka fatattaka daga kan iyakokin Siriya da Labanon ba su da wata mafita face kawai su mika kansu ga dakarun gwagwarmaya.
-
HKI Ta Yi Barazanar Kai Hari Kan Fadar Shugaban Kasar Siriya
Aug 28, 2017 14:31Wani jami'in gwamnatin HKI ya ce idan jumhoriyar musulinci ta Iran ta ci gaba da karfafa matsayinta a siriya, to isra'ila za ta yi lugudar wuta a kan fadar shugaban kasar Siriya.
-
Kananan Yara Palastinawa 400 Ne Isra’ila Ke Tsare Da Su A Gidan Kaso
Aug 28, 2017 07:55Rayyad Ashqar mai magana da yawun cibiyar Palastinawa mai kula da fursunonin da haramtacciyar kasar Isra’ila take tsare da su yabbayana cewa akwai kananan yara 400 da suke tsare a gidajen kason Isra’ila.
-
Afganistan : Harin Taliban Ya Kashe Mutum 13
Aug 28, 2017 00:29Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane 13 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da wani dan Taliban ya kai da mota kan wani ayarin motocon soji a kudancin kasar.