-
Gwamantin Syria Za Ta Maida Martani Kan Harin Homs
Feb 25, 2017 13:08Gwamanatin Syria ta sha alwashin maida martani mai tsanani kan harin da tsohuwar kungiyar reshen Al'Qaida ta kai a birnin Homs wanda ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 40.
-
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Ya Ziyarci Iraki, Karon Farko Tun 2003
Feb 25, 2017 12:05Ministan harkokin wajen Saudiyya, Adel al-Jubeir, ya fara wata ziyara aiki a kasar Iraki inda ya gana da mahukuntan kasar a wani yunkuri na farfado da alakar dake tsakanin kasashen biyu.
-
Yan Kasar Turkiyya 136 Ne Suke Neman Mafakar Siyasa A Kasar Jamus
Feb 25, 2017 03:08Gwamnatin Jamus ta sanar da cewa: 'Yan kasar Turkiyya da yawansu ya kai 136 kuma mafi yawansu masu dauke da takardar izinin tafiye-tafiye na jakadanci ne suke neman mafaka a cikin kasarta.
-
Babban Kwamandan Sojojin Amurka A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ya Kai Ziyara A Asirce Syria
Feb 25, 2017 02:21A daidai lokacin da ake sukan amurka akan komawa kauye guda wajen tattaunawar da ake domin shawo kan rikicin kasar Syria, babban kwamandan tawagar sojojinta a yankin Gagas ta Tsakiya ya kai wata ziyara a asirce a kasar Syria.
-
Shirin Karfafa Samuwar Yahudawa A Cikin Birnin Quds
Feb 24, 2017 09:07Haramtacciyar kasar Isra'ila ta ware kudi dalar Amurka miliyan 190 domin karfafa samuwar yahudawa a cikin birnin Quds da kewaye.
-
An Soki Gwamnatin Kasar Bahrain Kan Cin Zarafin Fararen Hula
Feb 24, 2017 09:06Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa ta soki lamirin masarautar kasar Bahrain kan cin zarafin fararen hula masu fafutuka ta siyasa a kasar.
-
Nasarar Dakarun hadin gwiwar Iraki a yammacin Mausil
Feb 24, 2017 02:20Dakarun hadin gwiwar Iraki sun hallka sama da 'yan ta'addar ISIS 50 a garin Tal'afar na yammacin Mausil
-
Shugaban Rasha Ya Jaddada Cewa Kasarsa Bata Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Siriya
Feb 23, 2017 14:43Shugaban Rasha ya jaddada cewa: Kasarsa bata tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Siriya iyaka dai tana taimaka mata a fagen yaki da ta'addanci.
-
Dakarun Gwamnatin Iraki Sun kwao Filin jirgin sama na garin Mausil daga yan tawaye
Feb 23, 2017 07:23Dakarun Gwamnatin Iraki sun samu nasarar kwace filin jirgin sama na garin Mausil daga hanun 'yan ta'addar ISIS.
-
Dakarun Yemen Sun Hallaka Na'ibin Babban Kwamandan Dakarun Gwamnatin Hadi Dake Samun Goyon Bayan Saudiyya
Feb 22, 2017 14:27Rahotanni daga kasar Yemen sun bayyana cewar dakarun kasar tare da hadin gwiwan dakarun sa kan kasar sun sami nasarar hallaka mataimakin babban kwamandan dakarun gwamnatin tsohon shugaban kasar Yemen din Abd Rabbuh Mansur Hadi kana kuma daya daga cikin manyan kwamandojin dakarun hadin gwiwan da Saudiyya take jagoranta Janar Ahmad Saif Al-Yafi'i tare da wani adadi na sojojin sa kai a wani hari da suka kai yankin Mocha.